Titus 1

1Wasiƙa daga Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah—  2duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun filʼazal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi, 3da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin waʼazin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu.

4Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya:

Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu.

Aikin Titus a Kirit

5Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka. 6Dole dattijo yǎ kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ʼyaʼyansa masu bi ne waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba. 7Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yǎ zama marar aibi-ba mai girmankai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8A maimakon haka dole yǎ zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. 9Dole yǎ riƙe tabbataccen saƙon nan kan-kan yadda aka koyar, don yǎ iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yǎ kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.

10Gama akwai ʼyan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. 11Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba— don neman ƙazamar riba. 12Wani daga cikin annabawansu ma ya ce, “Kiritawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye haɗamammu.” 13Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsauta musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya, 14ba za su kuma mai da hankalinsu ga tatsuniyoyin Yahudawa ko ga umarnan waɗanda suke ƙin gaskiya ba. 15Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne. 16Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.

Copyright information for HauSRK